Sunday, 16 December 2018

Southampton ta taka wa Arsenal burki da ci 3-2

Southampton ta ci Arsenal 3-2 a wasan mako na 17 a gasar Premier da suka kara a St Mary a ranar Lahadi.


Southampton ce ta fara cin kwallo ta hannun Ings minti 20 da fara wasa, kuma minti takwas tsakani Arsenal ta farke ta hannun Mkhitaryan.

Daf da za a je hutu ne Ings ya kara na biyu, sannan Mkhitaryan ya kare farke kwallo, saura minti biyar lokaci ya cika ne Austin ya ci wa Southampton kwallo na uku.

Da wannan sakamakon Southampton ta takawa Gunners burki kan buga wasa 22 a jere ba tare da an doke ta ba.

Haka kuma Southampton ta koma ta 17 a kasan teburi da maki 12, ita kuwa Arsenal tana ta biyar da maki 34.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment