Friday, 7 December 2018

Tambuwal Ya Yi Raddi Ga El Rufa'i

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya yi ikirarin cewa takwararsa na jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i ya razana ne kan yadda ya ga dandazon jama'a a wurin bikin kaddamar da yakin zaben Atiku Abubakar wanda aka yi a Sokoto.

Tambuwal ya ce, bai yi mamaki bisa kalaman El Rufa'i wanda ya nuna cewa mafi yawan wadanda suka halarci taron PDP a Sokoto duk 'yan kasar Nijar ne inda Tambuwal ya kara da cewa salon mulkin APC ce ya sanya mutane suka gujeta ganin yadda ta talauta jama'ar kasa.
Rariya.

No comments:

Post a Comment