Wednesday, 26 December 2018

Toni Kroos Ya Kafa Tarihin Da Babu Irinsa A Duniya: Ya zarta Ronaldo da Messi

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Toni Kross, shi ne na daya a yawan lashe kofin Zakarun nahiyoyin duniya a kungiyar, inda yake da biyar jumulla bayan kungiyar ta lashe kofin a wanna satin.


Dan kwallon tawagar Jamus ya yi nasarar lasher na biyar ne, bayan da Real Madrid ta doke Al Ain mai masaukin baki a birninAbu Dhabi na kasar Dubai a ranar Asabar din data gabata.

Hakan ne ya sa ya dara Cristiano Ronaldo mai guda hudu tare da Sergio Ramos da Marcelo da Carbajal da Isco da Bale da Benzema da Barane da Keylor Nabas da Nacho da kuma Modric.

Kross ya fara cin kofin Zakarun nahiyoyin duniya a shekarar 2013 a lokacin da tsohuwar kungiyarsa ta Bayern Munich ta doke Raja Casablanca, wadda tafito daga yankin Africa a wasan karshe .

Sauran hudun ya dauka ne a Real Madrid, wadda ya koma buga mata kwallo a shekara ta 2014 kuma har yanzu yana bugawa kungiyar wasa duk da cewa a kwanakin baya yaso barin kungiyar saboda wasu dalilai.
Leadershipayau.

No comments:

Post a Comment