Thursday, 20 December 2018

Tottenham ta fitar da Arsenal a Caraboa


Tottenham ta yi waje da Arsenal daga gasar Caraboa Cup, bayan da ta yi nasara da ci 2-0 a wasan da suka kara a ranar Talata.Tottenham ta fara cin kwallo ta hannun Son Heung-Min a minti na 20 da fara tamauala, sannan ta kara na biyu ta hannun Dele Alli bayan da aka dawo daga hutu.

Wannan ne wasa na 14 da kungiyoyin biyu suka fafata a League Cup, inda Arsenal ta ci karawa bakwai aka doke ta wasa hudu da canjaras uku.

Da wannan sakamakon Tottenham ta kai wasan daf da karshe a gasar ta Caraboa ta bana, ita kuwa Arsenal sai dai ta tara badi.

A ranar 2 ga watan Disamba ne Arsenal ta doke Tottenham 4-2 a wasan Premier da suka fafata a Emirates.

A karshen makon nan ne Southampton ta kawo karshen wasa 22 da Arsenal ta yi a jere ba a ci ta ba, inda ta yi nasara da ci 3-2 a kanta.

A daya wasan daf da na kusa da na karshe Chelsea ta yi nasarar doke Bournemouth da ci daya mai ban haushi.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment