Tuesday, 25 December 2018

Tsakanin General BMB da wani da yace mai be kamata ya bayar da lambar wayarshi a bainar jama'a ba

Wani ya ja hankalin tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB bayan da aka tambayeshi lambar wayarshi ya kuma bayar ta dandalinshi na sada zumunta da cewa be kamata ya bayar da lambarshi haka a idon Duniya ba, kamata yayi ya bayar a asirce.


Bello ya bashi amsar cewa,lallai ka yi tunani me kyau, amma ban ga wata matsala ba a bayar da lambar wayata ga mutane ba, babban burin dan fim kamin ya shiga harkar fim shine ya samu karbuwa a gurin mutane.

Amma bayan sun cimma burinsu sai su fara share masoyan su.

No comments:

Post a Comment