Wednesday, 26 December 2018

Tsakanin Hadiza Gabon da wani da ya hango gunki a wani hoto da ta saka

Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta saka wannan hoton na abokiyarta a dandalinta na sada zumunta inda masoyanta suka yaba saidai wani ya hango wani abu a hoton da yace a rinka kulawa.Bawan Allahn yace, Amma fa yar uwa naga kamar wani gunki ne a gaban madubi din adai ringa kula.

Wani ya bashi amsar cewa to ita ina ruwanta da abinda aka aje koma menene.

Hadizar ta rufa mai baya da cewa, kasan kowa sai ya nuna ya fika sanin addini.

No comments:

Post a Comment