Monday, 24 December 2018

Tsohon dan takarar shugaban kasa na APC ya koma PDP

Tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, Chief Charles Udeogaranya, ya fice daga jam'iyyar zuwa PDP.

Chief Charles Udeogaranya, ya fice daga APC dinne a wani taro da ya gudana a Legas inda ya bayyana cewa ya samu amincewar mutanenshi kamin ya koma PDP, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

Ya kuma kara da cewa, sabuwar jam'iyyarshi ta PDP zata fitar da 'yan Najeriya daga kangin tattalin arziki da sauran matsaloli da suke ciki.

No comments:

Post a Comment