Saturday, 1 December 2018

Tsohon shugaban Amurka George Bush ya mutu

Tsohon shugaban Amurka George Bush ya mutu yana da shekara 94 da haihuwa. Dansa George W Bush ne ya fitar da wannan sanarwar.


Tsohon shugaban da aka fi sani da George Bush Senior ya mutu ne ranar Jumma'a da yamma kamar yadda wani kakakin iyalin gidansa ya bayyana.

Shi ne shugaban Amurka na 41 tsakanin shekarar 1989 da 1993 bayan ya shafe shekara takwas a mukamin mataimakin shugaban kasa Ronald Reagan.

Amma duk kasancewa farin jininsa ya kai kashin 90 cikin 100, an tuhume shi da rashin kulawa da harkokin cikin gida, inda Bill Clinton ya kayar da shi a zaben 1992.

Ya taba zama matukin jirgin yaki a lokacin yakin duniya na biyu kafin daga baya ya shiga siyasa a 1964 a karkashin jam'iyyar Republican.

A watan Afrilu aka kwantar da shi a wani asibiti bayan da ya kamu da rashin lafiya, lamarin da ya faru mako guda bayan mutuwar matarsa Barbara.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment