Saturday, 1 December 2018

Ummi Zeezee ta wa wani masoyinta alkawarin tukwicin Naira dubu 100 bayan da ya mata alkawarin wata kyauta

Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta wa wani masoyinta alkawarin tukwicin kudi har Naira dubu 100 bayan da ya mata alkawarin bata wata kyautar da take matukar so.Ummi ta bayyana cewa cikin kyautuka tana girmama kyautar turare.

Sai wani ya bayyana mata cewa, ina fatan idan na kawo miki kyautar zaki karba, yace zai iya yin takakkiya yaje garin Kano dan ya bata kyautar.

Da yake masu iya magana sunce yaba kyauta tukwici, Ummi ta bashi amsar cewa, ta gode kuma idan ya bata kyautar ita kuma ta yi alkawarin zata bashi tukwicin Naira dubu 100.

No comments:

Post a Comment