Wednesday, 5 December 2018

United da Arsenal sun raba maki a Old Trafford

Manchester United da Arsenal sun raba maki a tsakaninsu, bayan da suka tashi 2-2 a gasar Premier wasan mako na 15 a Old Trafford.


Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hannun Mustafi minti 26 da fara wasa, inda United ta farke ta hannun Martial minti hudu tsakani.

Bayan da aka dawo daga hutu ne aka ci kwallo biyu a minti biyu, Arsenal ce ta kara zura wa a raga ta ta hannun Lacazette nan da nan United ta farke ta hannun Lingard.

Da wannan sakamakon Arsenal ta koma ta biyar kan teburi da maki 31, yayin da United ta yi kasa zuwa mataki na takwas da maki 23.

Manchester United za ta karbi bakuncin Fulham a ranar Asabar a Old Trafford, inda Arsenal za ta kara da Huddersfield Town a Emirates a ranar ta Asabar 8 ga watan Disamba.

Sakamakon wasu wasannin mako na 15 da aka yi.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment