Saturday, 8 December 2018

Wani mutum wanda shi kadaine musulmi a wani kauye ya zama shugaban kauyen ba tare da hamayya ba

Wani abin ban sha'awa da birgewa ya faru a kauyen, Bhelan-Kharothi dake Hanga Panchayata kasar India inda wani mutum me suna Mohammad Hussain wanda daga shi sai iyalinshine kawai musulmi a kauyen ya lashe zaben zama shugaban kauyen ba tare da hamayya ba.


Duk da yake cewa mutanen kauyen duk mabiya addinin Hindu ne amma sun amincewa Mohammad Hussain musulmi daya tilo ya zama shugabansu saboda sun bayyanashi da iya warware matsaloli da kuma halayya ta gari.

Sauran dalilan da suka bayyana na zaben Mohammad Hussain a matsayin shugaban su sun hada da nuna mishi cewa kada yaji wata tsangwama kasancewarshi shi kadaine musulmi a garin, kamar yanda Timesnownews ta ruwaito.

Wannan dai ya zo wa mutane da dama da ban mamaki ganin cewa, ana samun raashin jituwa tsakanin mabiya addinan biyu akai akai a kasar.

No comments:

Post a Comment