Monday, 3 December 2018

Wannan fa ba Buharin gaskiya bane>>Ini Nnamdi Kanu

Shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya mayar da martani akan maganar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi jiya a kasar Poland yayin da yake ganawa da 'yan Najeriya mazauna kasar.

Shugaba Buhari a jiya ya bayyanawa 'yan Najeriyar cewa, shine fa da kanshi, ba'a canjashi ba kuma wasu sun yi fatan dama ya mutu a lokacin da yayi jiyyar rashin lafiya.

Saidai Nnamdi Kanu ya bayyana cewa, shifa ba cewa yayi an canja Buhari ba ko kuma an kwaikwayi surarshi aka kawo wani wai me suna Jibrin daga kasar Sudan ba.

Ya kara da cewa, shi cewa yayi Buhari ya mutu, aka dauko shi wancan Jibrin din na kasar Sudan akan maye Buhari dashi, kamar yanda jaridar Independent ta ruwaito. 

No comments:

Post a Comment