Thursday, 27 December 2018

Wariyar launin fatar da aka nunawa Kalidou Koulibaly: Ronaldo ya nuna Alhini, magajin garin Milan ya bashi hakuri

A jiyane dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Napoli, Kalidou Koulibaly ya gamu da mummunar nuna wariyar launin fata daga magoya bayan kungiyar Inter Milan a wasan da suka buga.


'Yan kallon sun rika wa dan wasan ihun Biri a lokuta da dama da aka shafe ana buga kwallo, daga karshe dai an baiwa dan wasan katin gargadi saboda mugunta da yayi sannan saboda yabon shagube da ya yiwa alkalin wasan aka karamai kati na biyu ya zama jan kati, aka koreshi daga filin wasan gaba daya.

Kamar da ma shi ake jira ya fita aikuwa ana gab da tashi Inter din ta likawa Napoli kwallo daya me ban haushi aka tashi 1-0.

Bayan kammala wasa, me horas da kungiyar ta Napolin, Carlo Ancelotti yafi nuna damuwa akan abinda akawa dan wasanshi fiye da rashin nasarar da suka samu a wasan.

Carlo Ancelotti ya bayyana cewa, abin takaicine da aka kwashe daukacin lokacin buga wasan ana wa dan wasan bayanshi nuna wariyar launin fata ta hanyar haushin biri.

Yace dan wasan nashi ya kasance me nutsuwa da kuma yin aiki bisa ka'ida amma abinda aka mishine yasa ya shiga cikin wani hali.

Yace sau uku ana sanarwa ta amsa kuwwa cewa shi, ya bukaci a tsayar da wasan amma aka kiya aka ci gaba ana gaya musu cewa za'a dakatar da wasan.

Yace nan gaba idan haka ta sake faruwa zasu dauki doka a hannunsu, barin wasan kawai zasu yi duk da cewa sun san idan suka yi haka za'a basu rashin nasara a wasan amma basu da zabi.

Ya kara da cewa wannan ba abubane me kyau ga kwallon kasar Italiya ba.

Bayan kammala wasan, Kalidou Koulibaly ya saki sako ta shafinshi na Twitter inda yace be ji dadin rashin nasarar da suka yi ba amma abinda ya fi bashi haushi shine barin abokan wasanshi da yayi a cikin fili.

Yace amma yana alfahari da kalar fatarshi da kasancewa dan Faransa da kuma Senegal da dan wasan Napoli.

Tauraron dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo ya nuna alhini akan abinda akawa Kalidou Koulibaly inda ya saka wancan hoton na sama sannan ya rubuta cewa, akwai bukatar ilimi da girmama juna aharkar kwallo da Duniya baki daya, nuna wariyar launin fata be kamata ba, nuna banbanci be kamata ba laifi be kamata ba.

Shima a sakon da ya fitar,magajin garin Milan, Sala ya ce abinda akawa Kalidou Koulibaly be dace ba kuma a madadinshi da birnin Milan yana baiwa dan wasan hakuri.

Sala wanda shima yaje kallon wasan na jiya ya bayyana cewa nan gaba idan irin haka ta sake faruwa to zai fita ya bar filinne kuma duk wanda ya sake yin irin wannan abu ya nuna mai shima baya girmamashi.

No comments:

Post a Comment