Sunday, 23 December 2018

'Ya kamata 'yan Majalisa su nemi afuwar 'yan Najeriya'

Kungiyar Daliban Najeriya NANS ta bukaci ‘yan majalisun Najeriya da su nemi afuwar ‘yan kasar dangane da rashin nutsuwa da dattako da wasunsu suka nuna a  yayin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ke gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019.


Kungiyar wadda ta soki halayyar ‘yan majalisun ta hannun kakakinta Mista Adeyemi a garin Abeokuta, ta zargi ‘yan majalisun da zubar da kimar Najeriya a idanun duniya.

Kungiyar daliban ta kalubalanci ‘yan majalisun Najeriya da su rika fifita kimar kasar da shugabanta da kuma talakawa fiye da san zuciya ko ra’ayinsu na siyasa cikin kowanne hali.

A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a gaban ‘yan majalisun dattawa da na wakilan kasar, in da wasunsu suka rika ihun nuna masa adawa, yayin da wasu ke ihun goya masa baya a daidai lokacin da yake tsaka da bayani, lamarin da ya sa shugaban jan hankalinsu da cewa duniya na kallon abin da ke wakana.

No comments:

Post a Comment