Saturday, 22 December 2018

Yadda aka lallasa Man City da Chelsea a gida

Manchester City ta sha kashi a gidanta 3-2 a hannun Crystal Palace, yayin da Leicester City ta doke Chelsea 1-0 a Stamford Bridge.


Karon farko ke nan a shekaru kusan 26 da Palace ta samu nasara kan Manchester City a gidanta.

Wannan kuma ya kara dakushe burin Manchester City na kare kofin Firimiya da ta lashe a kakar da ta gaba.

Manchester City ce ta fara zuwa kwallo a raga, daga baya kuma Crystal Palace ta rama kuma ta sake zurara wasu kwallayen a ragar City.

Yanzu Liverpool ta kara ba Manchester City tazarar maki hudu a teburin Firimiya bayan ta doke Woles 2-0 tun a ranar Juma'a.

Liverpool, wacce kusan a kaka uku a baya tana dare wa teburin Firimiya amma ba tare da lashe kofin gasar ba, yanzu tana da maki 48 a wasa 18, makin da Chelsea ce kawai a kakar 2005-06 da kuma Manchester City a bara suka taba samu kafin rabin kaka.

Jamie Vardy ne ya taimaka wa Liecester doke Chelsea inda ya kawo karshen wasa uku a jere da Leicester ke kai ziyara Stamford Bridge tana fita ba nasara.

Nasara ta biyu ke nan da Leicester ta samu a wasanni shida da ta buga a Firimiya.

A daya bangaren kuma, Arsenal da ke matsayi na biyar a tebur ta casa Burnley ne 3-1 a Emirates.

Rashin nasarar da Manchester City da Chelsea suka yi wata dama ce ga Manchester United domin rage yawan makin da ke tsakaninsu idan ta doke Cardiff.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment