Sunday, 2 December 2018

Yanda ake shagalin Auren Priyanka da Nick: Sun zama Ango da Amarya: Priyanka tace tana so ta haihu da yawa

Bayan da aka sha shagulgulan kamin biki wanda ya samu halartar dangin Ango da Amarya, a Jiya Asabar an daura auren tauraruwar fina-finan kasar Indiya, Priyanka Chopra da Nick Jonas bisa koyarwar addinin Kiristanci.A ranar farko da Nick Jonas ya fara ganin Priyanka durkusawa kasa yayi kan gwiwoshinyi ya gaya mata cewa, kece amma ya aka yi kika dade baki zo ba? Na yi ta jiranki tsawon rayuwata, inji Vogue.

Akwai banbancin shekaru 10 tsakanin ma'auratan inda Priyanka ke da shekaru 36 shi kuma Nick na da shekaru 26.

Bayan daura auren nasu, an rika buga irin wutarnan me tashi sama tana tartsatsi, saidai da dama daga cikin mabiyanta a shafukan sada zumunta sun soki Priyankar inda sukace a baya fa itace ke cewa bai kamata ana amfani da wuta me tartsasti a wajan shagulgula ba.

A wata hira da jaridar Vogue ta yi da Priyankar ta bayyana cewa, Burinta shine ta haifi yara, tace tana so ta haihu da yawa.

A yau, Lahadi ne, 2 ga watan Disamba za'a kuma daurawa ma'auratan aure bisa koyarwar addinin Hindu.


No comments:

Post a Comment