Tuesday, 4 December 2018

Yanda Samari 'yan karya suka fi daukar hankulan 'yan matan Arewa

Wani bawan Allah ya bayyana irin yanda samari 'yan karya suka fi daukar hankulan 'yan matan Arewa akan masu sonsu tsakani da Allah.


Yace, Budurwa 'yar Arewace saurayi zai yi wata uku yana zuwa gurinta da motoci daban-daban sai tace, Ashema bashi da mota ko daya. To wallahi na gaji da yan karya. Ina bukatar me sona tsakani da Allah.

Ya kara da cewa, amma da ta samu me son nata tsakani da Allah ta ganshi a Keke Napep/ Adaidaita Sahu sai ta fece.

No comments:

Post a Comment