Saturday, 8 December 2018

Yaro masoyin Messi ya shiga halin ni 'yasu

Murtaza Ahmadi dan kasar Pakistan, yaronnan masoyin tauraron dan kwallo, Lionel Messi wanda a shekarar 2016 hotunan shi suka watsu a Duniya sosai ta yanda har Messin ya gayyaceshi filin wasa suka dauki hoto tare a yanzu yana gudun hijira tare da mahaifanshi bayan da mayakan Taliban suka sasu gaba.


A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP yayi da mahaifiyar tashi ta bayyana cewa, mayakan taliban sunsha alwashin sai sun hallaka dan nata ba tare da ya musu wani laifi ba.

Yaron wanda yanzu shekarunshi 7 a Duniya ya bayyana cewa, shi burinshi ya kasance tare da Messi yan so ya koma zama dashi.


No comments:

Post a Comment