Wednesday, 12 December 2018

YAWAN SHEKARUN KO AURI-SAKIN?

Labarin Magidanci a garin Lapai da ke jihar Neja, Yakubu Chanji, ya auri budurwa 'yar shekara 15. Ya zama babban labarin da ya janyo muhawara gami da cece-kuce. 


A ra'ayin wasu na ganin morewar budurwa ta auri saurayi da karfinsu ya zo daya zai nuna mata soyayya da wasanni. Amma Dan shekara 70 ya auri 'yar 15 tazarar shekaru 55 sun yi matukar yawa. A lokacin da mace ta kai 30 ne ta ke kan ganiyar bukatar kusancin da Namiji. Hakan na nufin a yayin da ta kara shekaru 15 tana 30 shi kuma yana 85, wanda kowa ya san Dan 80 ba mace ce a gaban sa ba. 

Yayin da masu goyon bayan lamarin ke ganin gara auren wuri da zinar wuri. 

Sai dai idan abinda Jaridar DAILY NIGERIAN suka ruwaito cewa, ana kiransa Chanji ne sakamakon auri-saki da ya ke yi. Wannan shine abin damuwar, domin rahoton ya kawo cewar wani ya ce "A iya sani na yayi aure kusan sha biyu wasu sun ce ashirin, shi dai ba ya zama da mace sai guda hudu, yana sakin wata zai karo wata".

In dai gaske ne haka ya ke, akwai babbar matsala dattijo mai shekaru 70 ya rika aure yana saki har ya zamana an masa lakabi da wannan halayya. A addinance Allah Ya la'anci Mace ko Namijin da suke aure kawai domin dandane. Ka auri mace idan ka gama jin dadin saduwa da ita ka saki ka auro wata. Ko mace ta rika aure tana danadana namiji ta fita ta auri wani don shima ta danadana shi. 

Auren wuri ya danganta da a ina ne kuma wanne gida ne. Kowa da Matar aurensa kamar yadda kowa ya san gidan da zai je neman aure da Inda ba zai je ba. 

Yarinya da ta yi biyayya ga Iyayenta ta auri mai shekaru 70 Allah Ya ba ta ladan hakuri da juriya na bin iyaye. Su kuma iyayen Allah Ya na kallon niyyar su ta yin hakan. Idan sun nufi Allah ne da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Allah Ya saka musu da mafi Alheri. Idan kuma sun bi son zuciya 'ya'ya amana ne daga Allah zai kuma tambaye su kiwon da Ya ba su ranar Alkiyama. 

Ga Malam Mai Chanji matukar da gaske haka ka ke ka ji tsoron Allah ka daina wannan mummunar Dabi'a. Allah ne kadai Ya san halin da iyaye ke shiga yayin da aka sako musu 'ya'ya. Da kuma su kansu matan halin da suke kasancewa a yayin zawarci. Musamman ma ga mazan da ke sakin mata su kuma ki daukar dawainiyar 'ya'yan su.
Daga Maje El-Hajeej Hotoro.

No comments:

Post a Comment