Wednesday, 26 December 2018

Zan ci gaba da tafiya sannu a hankali har saina kwato duk kudaden da aka sacewa Najeriya>>Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya  jaddada cewa duk da akwai masu sukar gwamnatinshi da cewa tana tafiyar hawainiya amma zai ci gaba da tafiya sannu a hankali har sai yaga an kwato kudaden da barayin gwamnati suka sace.


Shugaban ya bayyana hakane a fadarshi ta Villa dake Abuja, jiya, Talata yayin da wasu mazauna birnin Abujan suka kaimai gaisuwar Kirsimeti, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Buhari ya kara da cewa, jam'iyyarshi ta APC ta tsayar dashi takara kuma bazai yi kasa a gwiwa ba zai ci gaba, yace alkawuran da suka yi a shekarar 2015 sune yaki da cin hanci, tsaro da habaka tattalin arziki.

Ya kara da cewa, sun yi kokari ta dukkanin fannonin, inda yace maganar tsaro mutanen Arewa maso gabas zasu bayar da shaida sannan ta bangaren tattalin arziki sun yi magananin rashin aikin yi inda yace mutane sun koma gona kuma an samu abinci.

Ta bangaren yaki da cin hanci kuwa yace ya bayar da labarin abinda yayi lokacin yana soja amma yanzu tunda tsarin Dimokradiyya ake sai an kama mutum an kaishi kotu an kuma gabatar da shaidu to shiyasa ake ganin abin na tafiyar hawainiya bawai lafinshi bane, tsarin kasarne a haka kuma zai ci gaba da wadannan alkawura.

Ya kara da cewa har yanzu maganar tsaro na nan dan saida tsaro za'a iya gudanar da mulki.

No comments:

Post a Comment