Thursday, 27 December 2018

Zan iya yin komai dan in same ka: Tsakanin wata budurwa data nace tana son wani saurayi shi kuma yace ta fita harkarshi

Wata baiwar Allah ta ja hankulan masu amfani da dandalin Twitter 'yan Arewa da akewa laqabi da ArewaTwitter cewa dan Allah su saka baki kamar yanda take bibiyar wani matashi shima ya biyota a shafinta dan kuwa tana sonshi.


Saidai mutumin ya mayar mata da amsar cewa, Salam babu bukatar hakan, saboda inada wadda nike so, kuma dan Allah ki fita harkata.

Saidai duk da wannan gargadi da ya mata taki ji, inda ta ci gaba da rokonshi da cewa, dan Allah karka min haka, na mato a soyayyarka, kuma zan iya yin komai dan in sameka.


No comments:

Post a Comment