Sunday, 16 December 2018

Zan kalli wasan Liverpool da Man U>Pep Guardiola

Me horas da kungiyar Manchester City, Pep Guardiola wadda a jiya ta koma saman teburin firimiya bayan nasarar da ta samu akan Everton ya bayyana cewa zai kalli wasa me muhimmanci a gareshi na tsakanin Liverpool da Man United.


Manchester City yanzu tana saman teburin Frimiya ne da maki biyu a gaban Liverpool kuma idan Liverpool ta yi nasara a akan Man U a wasan da zasu buga idan an jima to zata sake komawa saman teburin.

A lokacin da manema labarai ke hira dashi sun tambayi Pep Guardiola ko zai kalli wasan Liverpool da Man U? Sai yace kwarai kuwa wasa ne me daukar hankali, zan kalleshi.

No comments:

Post a Comment