Sunday, 6 January 2019

A karon farko likitoci sun samu nasaran yin tiyatar kwakwalwa (brain surgery) a asibitin kwararru na Muhammadu Buhari Specialist Hospital Kano

Maigirma Gwamnan jihar Kano Khadimul Islam ya ziyarci mutumin da aka fara yiwa tiyatar a karon farko cikin tarihi, kamar yadda zaku gani a hoto, irin wannan aiki da akeyi a kwakwalwar mutum yawanci sai an tafi kasashen waje, a dalilin haka mutane da dama cutar kansa na kwakwalwa tayi sanadin halakar dasu musamman talakawa.


Wannan babban cigaba ne aka samu a gwamnatin Baba Buhari Maigaskiya wanda talakawa zasu mora, kuma shine abinda gwamnatin PDP ta gaza yi a shekaru 16 da tayi tana mulkin kama karya tare da cin amanar 'yan Nigeria

Allah Ka taimaki shugaba Buhari Ka kara masa taimako da nasara akan 'yan jari hujja Amin.
Datti Assalafiy.


No comments:

Post a Comment