Thursday, 24 January 2019

Abin kunyane ace kasar Ghana ta shiga gaban Najeriya wajan jan hankalin 'yan kasashen waje masu zuba jari, zan gayara haka idan aka zabeni>>Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zabe me gabatowa, Atiku Abubakar ya bayyana takaicinshi akan yanda kasar Ghana ta kwacewa Najeriya kambun da take rike dashi na kasancewa cibiyar saka jarin kasashen waje ta kasashen yankin Afrika ta yamma.Atikun yace hakan ba karamin abin takaici bane ace kasar da duka-duka yawan jama'arta be wuce kashi 15 cikin 100 na jam'ar Najeriya ba amma ace wai ta shiga gaban Najeriyar wajan jan hankalin kasashen waje su zuba jari a cikinta. Atikun cikin wani rubutu da yayi a shafinshi na sada zumunta yace sakacin gwamnati me cine da kuma kunyata Najeriya da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rinka yi a ziyarar kasashen waje da yaje ne suka jawo wannan abu.

Kuma maimakon gwamnatin ta maida hankali kan gyara wannan matsala sai ta koma tana fada da wanda basa bin ra'ayinta kamar su alkalin alkalai.

Atiku yace idan aka zabeshi zai kwatowa Najeriya kambunta daga kasar Ghana sannan kuma zai samar da ayyukan yi saboda dama shi dan kasuwane yana kuma da fikirar kirkirar ayyukan yi.

No comments:

Post a Comment