Sunday, 6 January 2019

Adam A. Zango ya bayyana abubuwa 3 da yace sune kawai zasu sa ya daina sana'arshi

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango kenan a wannan hoton tare da abokin aikinshi, Morell, ya saka wannan hoton a dandalinshi na sada zumunta inda ya bayyana abubuwan da sune kawai zasu sashi ya daina yin sana'arshi.Adam A. Zango ya rubuta cewa, haka muke yi, haka muka iya, ta haka muke ci, ta haka muke ciyarwa. Hakane ya hanamu sata, hakan ne ya hanamu lalacewa. Ma'ana itace sana'armu shekara da shekaru kuma babu ranar dainawa sai dai idan abu daya a cikin uku ya faru.

Ko tsufa
Ko disashewar daukaka
Ko kuma mutuwa

Allah yasa mu cika da Imani.

No comments:

Post a Comment