Saturday, 12 January 2019

Alhaji Abdulsamad Rabi'u Dan asalin Jihar Kano a Najeriya ya zamo mai kudin Najeriya a mataki na uku (3) a shekarar 2019.

Jaridar Forbes Mai fitar jerin sunayen masu kudin Afrika a duk Shekara ta fitar da sunayen masu kudin Afrika na shekarar 2019 inda Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabi'u ya zamo na Uku (3) a Najeriya kuma na goma sha sida (16) Afrika 


Jaridar dai ta ruwaito Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabi'u mai kamfanin BUA dake sarrafa siminti da shinkafa da suga da cewar yana da jarin Dalar Amurka Biliyan daya da miliyan dari shida ($1.6B)

Inda Alhaji Aliko Dangote ya kasance a matakin farko.
Daga Real Sani Twoeffect Yawuri.


No comments:

Post a Comment