Friday, 11 January 2019

Ali Nuhu ya cika shekaru 20 a masana'antar Kannywood

Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu, Sarki na murnar cika shekaru 20 da fara yin fim a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood. Alin ya kasance a masana'antar fim din Hausa tun shekarar 1999.Ali Nuhu ya fito a fina-finai da dama da kuma bayar da gudummawa sosai a masana'antar Kannywood wanda dalilin haka ne yasa ake kiranshi da sunan Sarki, ya kawo jarumai da dama masana'antar wanda kuma suka daukaka, jarumai mata irin su, Rahama Sadau, Nafisa Abdullahi, da sauransu duk sun bayyana cewa Alin ne ya kawosu masana'antar.

Kusan indai a fim da Ali zaka ga jama'a na matukar so su kalleshi saboda irin farin jinin da yake dashi da kuma kwarewa a iya aiki.

Ali Nuhu ne na daya idan za'a jero fitattun jarumai na masana'antar Kannywood, ya dade tauraruwarshi na haskaka wa kuma da alama bashi da niyyar daina yin fim nan kusa.

Ali Nuhu na da mabiya sama da miliyan 1.5 a shafin Facebook sannan yana da mabiya sama da dubu 800 a shafin Instagram, yana kuma da mabiya sama da dubu 150 a shafin Twitter.

Kusan kowane jarumi yayiwa Ali Nubu mubaya'a da cewa shine sarkin Kannywood.

Muna tayashi murna da fatan Allah ya kara daukaka.

No comments:

Post a Comment