Tuesday, 8 January 2019

An baiwa Mourinhon aikin horaswa amma yace baya so


Jose Mourinho ya yi watsi da tayin da Benfica ta yi masa na zama sabon kocin ‘yan wasanta, abin da ya sa ake ganin har yanzu yana hangen daya daga cikin manyan fitattun kungiyoyi a nahiyar Turai.

Masana harkokin wasanni na ganin cewa, tsohon kocin na Manchester da Chelsea ba zai yi gaggawar komawa Portugal ba don ci gaba da aikin horarwa a dai dai lokacin da ludayinsa ke kan dawo.

Mourinho ya taba horar da Benfica a shekarar 2000 kafin daga bisa ya raba gari da ita bayan ya jagorace ta a wasanni tara a gasar Lig a Portugal.

A watan jiya ne, Manchester United ta sallami Mourinho daga bakin aiki bayan ya gaza kai kungiyar ga gaci.

A wata hira da ya yi da manema labarai a can baya, Mourinho ya ce, yana da makoma ta gari ba tare da Manchester United ba kamar yadda ita ma kungiyar ke da makoma ba tare da shi ba.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment