Tuesday, 8 January 2019

An fitar da Liverpool daga kofin FA

Kungiyar Wolverhampton Wanderers ta fitar da Liverpool daga gasar FA ta bana, bayan da ta yi nasara da ci 2-1 a fafatawar da suka yi a Molineux a ranar Litinin.


Wolverhampton ce ta fara cin kwallo ta hannun Raul Jimenez a minti na 38 ana murza leda, sai dai minti shida da aka koma wasa daga hutu ne Divock Origi ya farkewa Liverpool kwallo.

Minti hudu tsakani Wolverhampton ta kai zagaye na hudu a gasar FA, bayan da Ruben Neves ya ci kwallo na biyu.


Liverpool ta buga karawar da matasan 'yan kwallo domin ba su damar haskakawa.

Liverpool wadda take ta daya a kan teburin Premier bana ya rage mata kofin Zakarun Turai da take buga wa wato Champions League, bayan da aka fitar da ita a Caraboa.

No comments:

Post a Comment