Monday, 7 January 2019

An Yi Garkuwa Da Wani Basarake A Jihar Katsina

An yi garkuwa da wani Basarake, mai suna Babangida Lawal wanda shine Dagacin kauyen Zandar dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.


Majiyarmu ta 'Daily Trust' ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da Basaraken ne a daren jiya.

An yi garkuwa da Basaraken ne tare da wani dan kasuwa a kauyen mai suna Murtala Rabe.

Majiyar ta kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun kuma kara gaba zuwa wani kauye mafi kusa inda suka yi awon gaba da shanu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya kara da cewa suna iya kokarin su domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su din.

Idan a ba manta ba dai, a makon da ya gabata ne Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa wasu sassa na jihar Katsina na fama da 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane.
Rariya.


No comments:

Post a Comment