Friday, 11 January 2019

Ana neman karin mutane 13 bisa hannu a kisan Idris Alkali

Jiya, Alhamis 10-1-2019 Rundinar 'yan sandan Nigeria reshen jihar Pilato ta fitar da sabon sanarwa na neman wasu mutane 'yan kabilar berom mutum sha-uku (13) ana nemansu ruwa a jallo game da kisan Manjo Janar Idris Alkali


Cikin mutanen da rundinar 'yan sandan ta fitar da sanarwan nemansu ruwa a jallo mutum 13, 12 daga cikinsu sun fito daga kauyen Dwei ne dake gundumar Du, mutum 1 cikon na 13 ya fito daga kauyen Gushen a karamar hukumar Jos ta kudu

Ga sunayensu kamar haka:-
-Kannan Nyam 
-Solomon Gyang Jang
-Dustine
-Dung Deme
-Gyang Murrak
-Chuwang Samuel
-Nyam Samuel
-Dung Gbeh
-Daddy Dogo
-James Dung
-Gyang Dung
-Jay Boy

Maimagana da yawun rundinar 'yan sandan jihar Pilato DSP Mathias Tyopev yace; ayyana wadannan mutane da akayi a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo ya biyo bayan sabon bincike da rundinar 'yan sandan take cigaba da gudanarwa game da kisan Janar Idris Alkali, wanda hakan yasa ta gano suna da hannu dumu-dumu a ciki wajen kisan Janar din

Rundinar 'yan sanda reshen jihar Pilato tana rokon jama'a duk inda akaga wani mai suna irin na wadannan da aka lissafa a sama ayi kokarin kaiwa rahoto zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa, ko kuma a kira wadannan nambobin waya kamar haka: 07059473022, 08038907662, 08075391844, 09053872296.

Jama'a a taimaka wajen yada sanarwa.
Muna rokon Allah Ya tona musu asiri a duk inda suka buya a wannan duniyar

Allah Ka sa kisan Janar Idris Alkali yayi sanadin kawo karshen ta'addancin berom a kudancin Jos Amin
Allah Ka jikanshi Ka kyautata makwancinsa Amin
Datti Assalafiy.


No comments:

Post a Comment