Wednesday, 23 January 2019

Atiku ba ma'asumi bane amma yafi Buhari nunkin baninkin>>Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa da ace zasu tonawa wadanda ke karkashin gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari asiri to ba gidan yari kadai zasu shigaba wuta ma zasu shiga.Obasanjon ya bayyana hakane a wata hira da yayi da BBC inda yace, wadanda ke mulki yanzu da za'a tona musu asiri da duk wuta zasu shiga, Ya kara da cewa duk da cewa Atiku ba ma'asumi bane amma idan aka lura da abinda ke wakana yanzu to da Atikun zai samu mulki sai yayi abinda yafi na Buhari ninkin ba ninkin.

Obasanjo yace, a baya ya gayawa 'yan Najeriya cewa, Buhari baida kwarewa a fannin tattalin arziki, shin basu ga hakan ba? Sannan kuma ya gaya musu cewa baida kwarewa wajan harkar hudda da kasashen Duniya, shima an gani a kasa, dan haka ya kamata a gaskata Shi


No comments:

Post a Comment