Thursday, 10 January 2019

Atiku yayi abin yabo: Me goyon bayan Buhari ya yaba mai sosai

Datti Assalafiy sanannen me goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buharine da ya dade yana kare muradun gwamnatin APC a shafukan sada zumunta, saidai a kwanannan bayan komawar abokin aikinshi, Rabiu Biyora bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, shima ya fara yabon Atikun.


Wannan kusan rubutu na biyu kenan da Datti yayi akan kare Atiku wanda har yasa wasu mabiyanshi suke ganin cewa anya shima Atikun bazai janye shiba?

Ga abinda ya rubuta a shafinshi na Facebook kamar haka:

WAZIRIN ADAMAWA #ALH_ATIKU_ABUBAKAR ALLAH YA SAKA MAKA DA ALJANNAH

Daga abokina Ahmad Galactico
Wani Abu ya kaini Filin Jirgin saman Qasa dake nan Abuja wato #NNAMDI_AZIKIWE_INTERNATIONAL_AIRPORT sai na hangi mutane curko curko, sai nace bari inje ingani da ido na.......

Ashe wai mutane ne mutum 5 za'a kaisu Kasar Waje (ABROAD) Magani basu da lafiya, cikin su babu mai iya yin komai da kanshi, na nemi IZININ daukan Hoton su masu kula da su basu Amince min ba

Ashe wai #BABA_ATIKU ne ya dauki NAUYIN su zuwa waje don nema musu lafiya, lallai Baba Atiku Arzikin ka na amfani, kaima Allah ya Tausaya maka a Ranar sakamako, kuma Allah ya biya ka da Aljannah

Da masu Arziki na irin wannan da NIGERIA ta ragu da Tallace Tallace da barace barace a NTA, AIT, CHANNELS da sauran su, Amma #NEXT_LEVEL_NIGERIA


No comments:

Post a Comment