Sunday, 13 January 2019

Ba wanda ya kai Messi cin kwallaye a Turai

Dan wasan tawagar Argentina da Barcelona, Lionel Messi shi ne na daya a yawan cin kwallaye a gasar lik-lik ta nahiyar Turai ta bana.


Dan wasan kyaftin din Barcelona ya ci guda 16 a La Ligar bana, har da wadda ya zura a ragar Getafe a ranar Lahadi da kungiyar Nou Camp ta yi nasara da ci 2-1.

Messi ya ci kwallo 16 a wasa 18 da ya yi a La ligar 2018/19, kuma kungiyoyi 10 ya zura wa kwallayen a raga.


Kyaftin din Argentina ya ci Getafe a farkon Janairun 2019, ya taba yin irin wannan bajintar a 2017 da ya zura kwallo a ragar Villareal da kuma Levante a 2018.

Messi yana da maki 32, da yake duk kwallo daya maki biyu keda ita, wanda yake mataki na biyu shi ne Liu mai taka leda a Kalju ta Estonia.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment