Sunday, 13 January 2019

BABBAN DARASIN DA NA KOWA A SIYASAR NIGERIA

A hakikanin gaskiya na kara fahimtar cewa 'yan siyasar Nigeria kusan halinsu daya ne idan ka cire shugaba Buhari
Kamar yadda Malam Albaniy Zariya yace; "..bama zagin wani 'dan siyasa kuma bama kushe shi, amma bamu yarda da kowa sai Buhari.."


Ni dai a yanzu na kara fahimtar yanayin tsarin siyasar Nigeria sakamakon canza sheka da wasu 'yan siyasa keyi daga wata jam'iyya zuwa wata domin neman mafaka a abinda suka aikata na cin amana ko satar dukiyar talakawa da sukayi, a lokacin da suke rike da madafun iko kafin a canza gwamnatinsu

Misali mutum ne yayi shugabanci ya tafi yabar bashi sama da naira biliyon dari har EFCC ta kama gida da wasu kadarorinsa, amma yau ya dawo jam'iyya mai mulki aka karbeshi tare da karramawa, har ma ya tsaya a gaban shugaban 'kasa yana rokon ya masa afuwa bisa abinda ya aikata na kuskure a baya

Shugaban jam'iyya mai mulki na 'kasa ya daga hannunsa yace barka da shigowa cikin jam'iyyar mu, yanzu mun zama daya, wannan ya nuna cewa maganar binciken da ake masa ya kare kenan, daga can gefe kuma sai ga wani kasurgumin mutumi wanda wakilin UN yayi  zarginsa da hannu wajen assasa kungiyar 'yan ta'adda tare da daukar nauyinsu, amma da ya canza sheka ya dawo jam'iyya mai mulki sai gashi yana zaune kusa da shugaban da duk duniya ta yadda Maigaskiya ne

Wannan itace tsarin siyasar Nigeria, hakika mun tabka kuskure a baya bisa zafafawa da muke akan wasu 'yan siyasar da basa tare da ra'ayin mu, yau an wayi gari na kara tabbatar da cewa duka halin 'yan siyasar Nigeria daya ne, kuma daga yau insha Allahu na dena zafafawa akan duk wanda ra'ayin siyasa bai hadamu ba

Allah Ka bamu mafita na alheri
Datti Assalafiy.


No comments:

Post a Comment