Sunday, 6 January 2019

Babbar Malamar Addinin Musulunci A'isha Lemu Ta Rasu

A yau, Asabar, 5 ga watan Junairu, 2019, Allah ya yi wa babbar malamar addinin Musuluncin nan 'yar asalin kasar Birtaniya, Bridget Aisha Lemu, rasuwa. Malamar ta rasu tana da shekaru 78 a duniya. 

Malama Bridget A'isha Lemu, wadda ta kasance fitacciyar marubuciyar littafan addinin M
usulunci, baturiyar kasar Birtaniya ce wadda ta karbi addinin Musulunci a shekarar 1961.

An haife ta a garin Poole na kasar Ingila a shekarar 1940. A'isha ta soma wasuwasi a kan addininta na farko tun tana shekaru 13. Hakan ne ya sa ta soma bincike a kan wasu addinai kamar addinin Hindu da kuma Buddha na kasar Chana. Ta yi karatu a jami'ar birnin Landan karkashin makarantar nazarin mutanen gabashin Asia da Afirka, 'School of Oriental and African Studies (SOAS)', inda ta maida hankali a bangaren tarihi, yare da kuma al'adun kasar Chana. A lokacin da take can ne ta hadu da wasu Musulmai da suka damka mata adabin addinin Musulunci domin ta karanta. Hakan ya sa ta karbi addinin Musulunci a cibiyar addinin Musulunci a shekarar 1961. 

Musuluntarta ke da wuya ta taimaka gurin kafa kungiyar mabiya addinin Musulunci a jami'ar, inda ta zamo sakatariyar kungiyar ta farko. Bayan nan kuma ta taimaka gurin kafa tarayyar kungiyoyin dalibai mabiya addinin Musulunci. 

Bayan kammala karatu a SOAS, Aisha Lemu ta koma digiri na biyu a bangaren koyar da yaren Turanci a matsayin yaren kasar waje. A lokacin da take karatun ne Allah ya hada ta da mijinta, Sheik Ahmad Lemu, wanda shima yake karatu a wata kwalejin jami'ar Landan, sannan kuma shima yake ayyukan yada addinin Musulunci a kwalejin. 

Bayan ta samu kwalin digirinta na biyu a fannin koyarwa sai ta taho jihar Kano ta kasar Nijeriya a watan Agusta 1966  domin ta yi aikin koyarwa a makarantar koyon yaren Larabci, inda Sheik Ahmad Lemu yake a matsayin shugaban makarantar. Sun yi aure a watan Afrilu, 1968, inda A'isha ta zamo matarsa ta biyu. Bayan nan A'isha ta koma Sakkwato inda ta zamo shugabar makarantar 'yan mata ta gwamnati.

A shekarar 1976 Sheik Ahmad Lemu ya zamo shugaban alkalan kotun daukaka kara ta addinin Musulunci a jihar Neja, yayin da Aisha take shugabar kwalejin mata da ke Minna. Ma'auratan sun kafa gidauniyar ilimin addinin Musulunci "Islamic Education Trust (IET)" wadda take da rassa a jihohin Nijeriya da dama. IET na da ofisoshi da dakunan karatu da cibiyoyin karatun manyan mata. A'isha ta kasance mamba na kwamitin ilimin addinin Musulunci, wanda hukumar bincike da bunkasa ilimi ta Nijeriya ta kafa domin yin bitar manhajar darasin ilimin addinin Musulunci na makaratu.

A shekarar 1985, A'isha ta samar da tarayyar kungiyoyin mata Musulmai (FOMWAN) inda aka zabe ta a matsayin Amirar kungiyar ta farko. Ta shafe shekaru hudu cur tana shugabantar kungiyar. 
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment