Saturday, 5 January 2019

Babu Adalci a rabon mukaman gwamnatin Buhari: Yawancin shuwagabannin tsaro 'yan Arewane kuma addini daya>>Atiku

Dan takarar shugaban kasa karkashin tututar Jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar yace babu adalci a yadda aka raba mukamai a gwamnatin Buhari.
A cikin hirarshi da Sashen Hausa na VOA, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriyan yace sa kabilanci da addini a harkokin mulki ko raba mukamai rashin adalci ne, kuma yana daga cikin babbar matsalar da ake fuskanta a Najeriya.

Da yake bayyana yadda zai tunkari wannan matsala, Alhaji Atiku yace idan shugaba ya yi adalci ya ba kowanne addini da kuma kowanne bangare hakinshi za a zauna lafiya. Yace “idan aka dubi shugabancin jami’an tsaron Najeriya gaba daya, kusan wajen mutum ashirin, a cikin wajen mutum ashirin din nan, wata kila mutum daya ne ko biyu daga kudu, sauran duk daga arewa ne, kuma a ce kusan yawancinsu addini guda. Kaga ba a nuna adalci a nan ba.”Alhaji Atiku yace dokokin Najeriya har ma da addini ya bukaci cewa, idan Allah ya baka shugabanci ka yi adalci.

Dan takarar shugaban kasar na jam’iyar PDP ya bayyana cewa, ana fama da yawan tashin hankali ne a arewacin Najeriya domin su ne suke da filayen noma kuma dabbobi a arewa suke. Sai dai ya bayyana rashin fahimtar abinda ya kawo fitina yanzu kasancewa an zauna tare kaka da kakanni lafiya. Yace tsame sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma na gargajiya a tsarin shiga tsakanin makiyaya da manoma yana daga cikin dalilan da suka haifar da rikicin manoma da Makiyaya. Ya kuma bayyana cewa matakin farko da zai dauka na shawo kan wannan matsalar idan ya zama shugaban kasa shi ne zaunawa da bangarorin domin fahimtar juna.

No comments:

Post a Comment