Sunday, 6 January 2019

Babu Kasar Duniya Da Aka Ci Amanarta Kamar Najeriya>>Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dake neman wa’adin mulki na biyu karkashin tutar Jam’iya mai mulki APC, ya bayyana cewa, babu kasa a duniya da aka ci amanarta kamar Najeriya, idan aka yi la’akari da abinda shugabannin gwamnatocin shekaru goma sha shida da suka shige suka yi.A cikin hirarshi da Sashen Hausa, shugaba Buhari yace wanda yake gani sheri ne ko kuma bita da kulli gwamnatinsa ke yi wa gwamnatin da ta gabace shi, yaje turai yaga yadda ake cinikin mai da kuma kudaden da ake samu, daga nan ya bayyana inda kudin su ke.Shugaba Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa bata iske komi ba a kasa.

Dangane kuma da kasafin kudin da ya gabatar gaban majalisa, shugaba Buhari yace, kasafin kudin shekara ta dubu biyu da goma sha tara da gwamnatinsa ta gabatar ya maida hankali a kan batun hanyoyi, da tsaro, da biyan ma’aika da kuma samar da wutar lantarki. Bisa ga cewarsa, kasar China ta amince zata yi wadansu hanyoyin mota da hanyoyin jirgin kasa, da dam-dam na Mambila, karkashin yarjejeniyar da aka kulla na biyan kashi goma sha biyar bisa dari na kudin da ake bukata, yayinda Najeriya zata biya sauran bashin cikin shekaru ishirin da ruwa kadan, Yace idan aka gaza samun tonon mai kamar yadda aka zata sai a sake duba hanyoyin da za a bi domin cike gibin da aka samu.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, yawanci basusukan da gwamnatinsa take biya ba ita ta ciwo su ba, ta gajesu ne daga gwamnatin da ta gabata.
VOAhausa.

No comments:

Post a Comment