Tuesday, 15 January 2019

BAMBANCIN SATAR APC DA PDP GUDA 10

1 Barayin PDP suna ci suna san wa talaka, na APC kuwa su kadai suke ci.

2 A PDP kowa barawo ne, Amma a APC shugaban kasa ba barawo bane.

3 A PDP kudi da ma'adinan gwamnati kawai ake sacewa Amma a APC har Dabino ana sacewa 

4 A PDP kasar waje ake kai kudin sata, amma a APC a babbar riga ake boyewa.

5 Barayin PDP sun cika bakin jini, Barayin APC kuwa talaka na son su 


6 A PDP mutum ake zargi da sata, amma a APC Jam'iyya ake zargi da sata.

7 A PDP in kana damawa da masu mulki ka tsira, amma a APC duk laifinka da ka shiga Jam'iyya ka hau tudun mun tsira duk satarka.

8  A PDP da aljihun gwamanati kawai ake kamfe, amma a APC har  aljihun talaka sai an kwakule.

9 A PDP barawo baya hada hotonsa da na me kama barayi don yayi kamfe, amma a APC Me kama barawo ke daga hannun barawo ya ce masa SAK

10 A PDP BARAWO ne kawai ke iya karya a majalisa, amma a APC Me gaskiya ke shararo karya.

Jama'a shin wannan hasashe na Rahma Abdulmajid zai iya zama gaskiya?
Daga Rahma Abdulmajid


No comments:

Post a Comment