Sunday, 6 January 2019

Bana cikin wanda suka wa Buhari ihu a majalisa>>Inji Dino Melaye bayan da 'yansanda suka kamashi

Sanata Dino Melaye ya nesanta kanshi da ihun da akawa shugaba kasa, Muhammadu Buhari a majalisar tarayya lokacin da ya je gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a watan disambar da ta gabata.A lokacin gabatar da kasafin kudin 'yan majalisar PDP sun rika wa Buhari Ihu wanda aka ruwaito cewa Dino Melayenne ya jagorancin yin ihun wanda har saida ta kai ga cewa Buharin ya dakatar da jawabin da yake ya gargadi  'yan majalisar cewa be kamata ba domin Duniya na kallonsu.

Saidai Dino bayan awa 24 da kamashi da 'yan sanda suka yi bisa hannu a yunkurin kisan dansanda ya fito ta hannun me magana da yawunshi, Gideon Ayodele, da yammacin jiya, Asabar ya karyata cewa yawa Buhari ihu.

Yace shi baya ma nan ranar da Buharin ya gabatar da kasafin kudin kuma idan akwai wanda ke da shedar cewa yayi hakan ya fito ya fada.

Ya kara da cewa, Dino ba mutum ne wanda idan yayi abu yake karyata kanshi ba.

No comments:

Post a Comment