Thursday, 24 January 2019

'Banda kyan fuska, matan hausawa basu iya soyayyaba, ba su iya kyakkyawar mu'amala ba da kuma kwanciyar aure'

Wani ma'abocin shafin Twitter ya soki matan Hausawa inda yace banda kyan fuska, basu iya soyayya ba, basu da kyakkyawar mu'amala sannan kuma basu iya kwanciyar aure ba.


Ya kara da cewa da yawansu in ka fara bibiyarsu a shafukan sada zumunta su ba zasu biyoka ba amma 'yan matan sauran yare ba haka suke ba.

Wasu dai sun yarda dashi yayin da wasu kuma suka kalubalanceshi.

A lokuta dama dama wasu na yin kuskuren yiwa mutane jam'i a yayin da mu'a malar da suka yi da wasu bata musu dadi ba, suce ai kabila kaza ga yanda suke ba tare da wata hujjar cikakken bincike ba, saidai kowa nada ra'ayinshi.No comments:

Post a Comment