Monday, 7 January 2019

Barcelona ta hada maki uku a Getafe

Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Getafe da ci 2-1 a wasan mako na 18 a gasar Spaniya da suka kara a ranar Lahadi.


Lionel Messi ne ya fara ci wa Barcelona kwallo a minti na 20 da fara tamaula, sannan minti 19 tsakani Luis Suarez ya kara na biyu.

Getafe wadda ita ce ta karbi bakuncin karawar, ta zare kwallo daya ta hannun Jaime Mata daf da za a je hutu.

Da wannan nasarar Barcelona ta na nan a matakinta na daya a kan teburin La Liga da maki 40.

Atletico Madrid ce ta biyu da maki 35, sai Sevilla da maki 33, sannan Deportivo Alves ta hudu da maki 31, sai Real Madrid ta biyar da maki 30.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment