Sunday, 6 January 2019

Bayanin Rabiu Biyora kan komawa goyon bayan Atiku daga gurin Buhari

TABBAS MUHAMMAD ATIKU ABUBAKAR YA ZIYARCENI.....

Bayani na farko.....

Ga duk mai bibiyar al'amuran da suka shafi wannan shafi nawa yasan cewa a wasu lokutan nakan bayyana cewa akwai matsalolin daya kamata a gyara a cikin siyasar da muke gabatarwa ta kare muraden jam'iyyar APC da Gwamnatin Shugaba Buhari, mukance koda aikin da muke don Allah ne da kuma kaunar gyara kasarmu hakan bazai hana a samar da wata kafar da zaa karawa matasan dake aikin kwarin gwiwa ba, wanda yin hakan zai kara musu fikira da nutsuwar tunkarar abokan adawa a kowanne lokaci, nassan kun san da haka.....


Bayanan da Biyora ya fitar game da sunayen mutanen da zasu taya shugaba Buhari kamfen a zabukan wannan shekara wadanda nake nuna damuwa akan kin saka sunayen mutanen da muke wannan aiki masu yawa daga nan Arewa, ya sanya hakan ya bada dama ga yan jam'iyyar Adawa ta PDP akan su gwada ko zasu samu mutanen da zasu amince suyi tafiyar siyasa dasu tunda dai baa saka su a inda suke ba...

Alhaji Muhammad Atiku Abubakar ya taso tun daga kasar France har zuwa nan Nigeria kai tsaye zuwa birnin Kano inda ya nemi a kirawoni mu tattauna, wannan karramawa ce a siyasance, tabbas mun tattauna har ya sanya in gayyato yan'uwana da abokaina don ya hadamun liyafar girmamawa domin yace bai kamata muyi tattaunawa dashi ba tare daya kyautatawa makusanta na ba....

Ya nemi da in tawo cikin kamfen din temakawa mahaifinsa musammam a wannan yanki namu na Arewa da kasa baki daya.....

GASKIYAR MAGANA.....

Zuwa yau din nan ban gama yanke kowacce shawara ba musammam dayake ina da iyaye, ina da yan'uwa sannan ina da matasa masu yawa da muke gudanar da wannan aiki tare dasu, wanda hakan yasa dole sai na tattauna da kowanne bangare kafin in yanke hukunci a wannan rana ko gobe.....cikin biyu dole ayi daya kodai na amsa wannan gayyata idan na samu goyon baya daga wadanda nake shawara dasu, ko kuma in zauna a inda nake, in sha Allah yau zuwa gobe zan yanke.....

Ina godiya sosai ga dukkan mutanen da suka nuna damuwa akan shaanin daya shafeni a siyasance, su kansu mutanen da suka kasa hakuri suka zageni ko aibatawa ina godiya garesu domin hakan da sukayi ya nuna cewa sun damu dani ne shiisa suka shiga damuwa akaina.....

MASHA ALLAH


No comments:

Post a Comment