Friday, 18 January 2019

Budurwar Pogba ta haifa mai jariri

Ga dukkan alamu tauraron dan kwallon kafar kasar Faransa me bugawa, Manchester United wasa,Paul Pogba ya zama uba bayan da labari ya samu cewa budurwarshi ta haifamai santalelen jariri.Da farko dai Pogba da budurwarshi, Maria Salaues basu so Duniya ta san da soyayyar su ba amma an fara ganin budurwar ta Pogba ne a wajan buga wasan cin kofin Duniya inda ta fito tana goyan bayanshi.

Sannan an ganta da cikin ta daya girma a wani wasan da ta zo kallon sahibin nata a lokacin bikin kirsimeti.

Sannan tsohon dan wasan Man U din, Bryan Robson ya bayyana cewa sun hadu shi da Pogba a birnin Dubai inda har ya mai murnar haihuwar da aka mishi.

Saidai har yanzu Pogba be tabbatar da wannan labari ba da kanshi.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa, an ga Pogba da budurwar tashi kwanaki biyu da suka gabata inda suka je cin abinci a wani kayataccen gidan cin abinci tare kuma ba'aga cikin nata da a da ya bayyana sosai ba.

Wannan yasa aka kara tabbatar da cewa budurwar ta Pogba ta haihu, saidai ko da aka gansu tare ba'a gansu tare da jaririn ba.

Wannan labari dai yasa wasu suka fara caccakar Pogba da cewa shi musulmine amma gashi ya haihu da mace ba ta hanyar aure ba.

Wasu rahotanni sunce Pogban har ya sayi wata tsaleliyar mota me dan karen tsada saboda murnar wannan haihuwa da aka mishi.

Sannan ko da abokan aikinshi suka tafi yin atisaye a Dubai Pogba be bisu ba sai daga baya yaje ya iske su acan, watakila haihuwar da aka maice ta tsedashi.

No comments:

Post a Comment