Friday, 4 January 2019

Buhari ya hada kai da gwamnonin Katsina da Zamfara dan su yi magudi a zabe me zuwa>>Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2019, Atiku Abubakar ya zargi cewa fadar shugaban kasa ta hada baki da gwamnonin jihohin Katsina da na Zamfara dan a yi magudi a zaben me zuwa.Atikun ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunshi, Phrank Shu'aibu inda ya fitar da sanarwar da ta bayyana cewa, Buhari da Gwamnan Zamfara sun yi taro a fadar shugaban  kasar a Abuja inda aka tattauna yanza za'a samarwa da APC damar cin zabe dan ta kayar da PDP.

Atikun yace duk da dadin bakin da Buhari yake yi na cewa wai zai gudanar da zabe na gaskiya amma a shirye yake yayi duk me yiyuwa dan ganin wancan kudirin na yin magudi a Zamfara da Katsina ya tabbata.

Atiku yace yana goyon bayan gwamnatin tarayya a shirin da take na kawo karshen rasa rayukan da ake samu a jihohin amma yana ganin saka dokar ta baci ba itace mafita ba, kamata ya nemo ainahin dalilin rikicin a maganceshi maimakon daukar matakin da zai sa 'yan ta'addan su canja waje.

No comments:

Post a Comment