Friday, 11 January 2019

Buhari ya kafa kwamitin daidaita albashin ma'aikata

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da wani sabon kwamiti da zai yi nazari kan ma’aikatan da ke karbar albashi mai tsoka fiye da ka’ida, da kuma zaftare albashin duk wanda aka samu akan tsarin.
Yayin kaddamar da kwamitin mai manbobi 24 a wannan Laraba, shugaba Buhari ya ba su wa’adin wata guda, su kammala aikin da aka dora musu, na gabatar da cikakken rahoto kan yadda gwamnati za ta aiwatar da karin mafi karancin albashin ma’aikata, da kuma hanyar samar da kudaden tabbatar da karin.

Matakin dai yunkuri ne na jifan tsuntsu biyu da dutse daya, wato kawo karshen rashin daidaiton albashin ma’aikata a Najeriya, matsalar da aka jima ana korafi akai, ta yadda ake fifita albashin wadanda ke aiki a wasu ma’aikatun fiye da na takwarorinsu, sai kuma warware takaddama tsakanin gwamnati da kungiyar kwadago kan batun karin mafi karancin albashi.

A watan Disamban da ya gabata, lokacin gabatar da kasafin kudin shekarar 2019, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi alkawarin kafa kwamitin da zai nazarci shawarwarin da kwamitin hadin giwa na gwamnati da na kungiyar kwadagon kasar NLC ya bayar, kan aiwatar da tsarin karin mafi karancin albashin ma’aikata.

Sai dai, a lokacin da sashin Hausa na RFI, ya tuntubi kakakin kungiyar kwadagon Najeriya Komrade Nasir Kabir, ya ce sabon kwamitin da aka kaddamar ba shi ne bukatarsu ba, abinda kawai suke son gani, shi ne a mikawa majalisun dokokin Najeriya kudurin neman karin mafi karancin albashin daga naira dubu 18 zuwa dubu 30, domin zama doka.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment