Friday, 4 January 2019

Ciwon Asamar Sanata Dino Melaiye ya tashi a ofishin 'yansanda

Wadannan hotunan sanata Dino Melaiye kenan yayin da ciwon asamar shi ya tashi a lokacin da ya shiga ofishin 'yansanda bayan mika kanshi da yayi.A cikin wani faifan bidiyo da gidan talabijin na Channels ya wallafa anga Dino Melaiye ana kakkamashi da kyar ya shiga ofishin na 'yansanda sannan kuma ya fadi kasa yana tari sai daga baya lauyanshi ya fito da magani yana bashi.


No comments:

Post a Comment