Thursday, 24 January 2019

DAN KWALLON NIJERIYA ABDULLAHI SHEHU YA TAIMAKAWA MATAN DA 'YAN FASHI SUKA YI WA MAZAJENSU KISAN GILLA A GARIN GANDI DA KAYAYYAKI

Shahararren dan kwallon Nijeriya kuma dan asalin jahar Sokoto Mai taka leda a kungiyar Busaspor dake kasar Turkiya, Abdullahi Shehu ya kaiwa mutanen da 'yan fashi suka yi wa mazajensu kisan gilla a satin da ya gabata a gundumomin Gandi da suka hada, Warwana, Tabanni da dai sauransu dake jihar Sokoto. Inda ya ba su tallafi domin bada tashi gudunmuwa ta hanyar tallafa musu. Wannan Taimakon Yazo adai dai lokaci da mutanen ke bukatar shi, duba da ganin halin da suka tsinci kansu cikin bazata, Wanda  yayyi sanadiyar mutuwar mutum ashirin da shidda. 

Wannan Taimakon an hannuntasa da hannun shahararren malamin Addinin Musulunci na jahar sokoto wato Malam Mansur Sokoto, domin ya jagoranci kai musu tallafin. 

Da yake jawabi a lokacin da tawagar ta kai masa wadannan kayayyaki da suka hada da, bargunan rufa, atamfofi, shaddodi, tabarmi da dai sauransu, ya yaba kwarai da gaske bisa wannan namijin kokarin da wannan Matashi ke yi, inda ya yi kira da ayi koyi da irin wannan halayen na kirki na dan kwallon.

Dakta Mansur Sokoto ya kara da cewa "ku sani wadannan abubuwa da Abdullahi ke yi na daga cikin ayyukan da Allah ke bukatar duk wani Bawa mai shi ya kasance yana aiwatarwa". 

Sannan ya roki Allah ya saka masa da alkairi bisa wannan aikin Allah da ya yi. Su kuma ya kara kare su daga afkuwar irin wannan.

Daga Aliyu Hungumawa Sak


No comments:

Post a Comment