Saturday, 12 January 2019

Duk da marigayi, Shehu Shagari ne ya aza tubalin ginin Abuja amma har ya sauka bashi da gida a cikinta

Babban dan marigayi, tsohon shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari, Kyaftin Muhammad Bala Shagari Sarkin Mafaran Shagari, mai shekara 69, ya bayyana cewa a lokacin da mahaifinsu ke shugaban kasa basu tafiya da jami'an tsaro, ya kuma bayyana yanda mahaifin nashi duk da cewa shine ya aza tubalin ginin Abuja amma bashi da gida a Abujan.Mubammad Bala Shagari ya bayyana hakane a cikin wata hira da Amniya ta yi dashi.

Ga abinda yace:

Wadanne abubuwa za ku rika tuna marigayin da su?

Abubuwan da za su sa mu rika tunawa da shi ba zan ce maka ga daya ba, domin suna da yawa amma dai ka sani bai koya wa ’ya’yansa girman kai da jiji-da-kai, wai su ji su ’ya’yan wani ne a kasar nan ba. Shi ne ya sanya muka zauna da mutane lafiya. Lokacin da yake mulki na sha tuka mota daga nan Sakkwato zuwa Legas, ba wani dan rakiya, babu wani dan gidanmu da ke yawo da wadansu matsara lafiyarsa, amma a zamanin yanzu ’ya’yan Shugaban Kasa in za su fita da ’yan rakiya suke fita. A lokacin da aka yi masa juyin mulki wani abokina ya same ni zan hau doki yake ba ni labarin cewa an yi juyin mulki. Na ce masa to me zan yi? Na ci gaba da sabgata. Ya tambaye ni wai ko ban yarda ba ne? Yana mamaki, ni ko a jikina, don tarbiyyar da ya ba mu ba ta barin mu dauki wani yana iya yin abin da Allah bai yi ba. Rayuwar marigayi abar sha’awa ce da kowa ke son yin irinta. Mun dauki koyarwarsa ta daya muke da kowa ba wani bambanci. Za ka ga abokanmu har wadanda ba su yi karatu ba, abokaina da muka taso tare da su cikinsu akwai makanikai da direbobi, haka muke zamanmu tare da su lafiya.

Ya kuma ce duk da mahaifinsune ya aza tubalin ginin Abuja amma har ya sauka daga mulki bashi da gida a cikinta.

Ga abinda yace akan hakan:

A Sakkwato kowa ya san kudirin marigayi na farfado da ilmi a jihar, za ku dora daga inda ya ajiye?

Za mu yi gwargwadon hali abin da muke iyawa, don ba mu iya cike gurbinsa. Rayuwar Turaki daban ce, shi ne ya dora tubalin ginin Abuja amma har ya sauka ba ya da ko fili a cikinta. Bayan an sake shi ne fa wani Babban Sakatare dan Nasarawa ya nemi ya zagaya da Turaki don ya ga ci gaban da aka samu a tubalin da ya dora. Bayan sun kammala ne yake tambayar Turaki ina gidansa? Yake fada masa ba ya da gida a nan nan fa. Ya ce ba za a yi haka ba. Ya bayar da fom a cika, ni na cika fom din na mayar. Koda na zo an dauke Babban Sakataren daga wurin. Na kai fom din wajen Minista Gado Nasko, shi ne ya ba shi fili a Abuja. An shekara 10 ba a gina komai a filin ba don ba ya da kudi. Obasanjo ne da ya zo ya gina masa gida a filin da aka ba shi. Shi kadai ne gidansa a Abuja. Dukanmu ’ya’yansa ba mu da gida a Abuja. In ka cire wadanda ke siyasa cikinmu.

No comments:

Post a Comment