Sunday, 13 January 2019

Garken Kudan Zuma sun kori mutanen wani gari a Filato

Garken Kudan Zuma sun tarwatsa mutanen kauyen Gunsun da ke karamar hukumar Kanam a jihar filato.


Sarkin Gunsun Idris Muhammad wanda ya tabbatar wa da BBC da faruwar al'amarin ya ce suna zaune da kusan 12 na ranar Lahadi suka ga garken kudan Zuma sun mamaye kauyen.

Ya ce nan take mutanen kauyen suka tarwatse, kowa ya ruga daji.


"Mutane da dama sun ji rauni, wasu ma sun karye a kafa," in ji shi.

Sai dai ya ce babu wanda ya mutu sakamakon yadda mutane suka firgita suna gudu zuwa daji.

Amma wani mazauni garin mai suna Ibrahim ya ce garken Kudan Zuma sun yi wa dabbobi da dama illa.

Mutanen kauyen dai na tunanin garken Kudan Zuma sun fito ne daga itacen Rimi da ke bayan gari.

Sun ce ba su san ko yara ne suka takale su ba, amma haka kawai suka ga sun mamaye gari.
Wasu kuma mutanen na tunanin asiri ne kamar turo wa mutanen kauyen aka yi da Zudan Zuma.

Sarkin garin ya ce hakan ta taba faruwa a 1998, inda garken Kudan Zuma ya kori mutanen gari kuma har an samu hasarar rayuka.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment